Makarantar fasaha ta Ungogo na neman ɗaukin gaggawa—Tsaffin ɗalibai

0
210

Wasu daga cikin tsofafin daliban makarantar fasaha ta kwana, dake kwanar Ungogo, sun nemi a kawo wa makarantar dauki daga gwamnatin jihar Kano, da sauran masu kishin ilimi.

Tsaffin ɗaliban da suka nemi a sakaya sunan su, sun bayyana takaici akan yadda suka ce an bar makarantar ta lalace tamkar ba ƴaƴan mutane ne ke yin karatu a cikin ta ba, duk da cewa bata yi nisa da kwaryar birnin Kano ba.

Sun ce akwai bukatar kawo daukin gaggawa a dakin kwanan dalibai da na karatu musamman rashin allon daukar darasi ga dalibai da bandakunan makarantar 

Daily News 24, ta rawaito cewa daga cikin ƙalubalen da makarantar ke ciki akwai rashin wajen zaman ɗalibai don ɗaukar darasi, rashin makewayi, da sauran abubuwan da zasu taimakawa koyo da koyarwa.

Akan haka ne tsaffin ɗaliban ke neman gwamnatin Kano ta tallafawa makarantar saboda gwamnatin tayi fice wajen inganta harkokin ilimi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here