Hukumar tace fina-finai ta Kano ta gamsu da bin dokokin ta a lokacin bikin babbar Sallah

0
60

A yayin bukukuwan Sallah Babba da aka gudanar a Jihar Kano, hukumar tace Fina-Finai da Dab’i ta bayyana gamsuwarta da yadda mamallaka dakunan taro da gidajen wasanni suka gudanar da harkokinsu cikin tsari da bin doka.

Bayanin hakan ya fito daga bakin Shugaban Kwamitin sa ido kan harkokin guraren wasanni, Alhaji Lawan Hamisu Danhassan, wanda shi ne Daraktan sashin fina-finai da cigabansa na hukumar.

 Ya ce dukkan wuraren da aka kai ziyara sun bi ka’idodin da hukumar ta shimfida domin kare tarbiyya da tsaftar al’umma a lokacin shagulgulan Sallah.

Hukumar mu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an ci gaba da bin doka. Za mu dauki mataki a kan duk wanda ya karya doka, ko da da sani ne ko rashin sani, in ji Danhassan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here