Ya kamata yan sandan Kano su rika nuna kwarewa a aikin su—Kwankwaso

0
168
Rabiu-Musa-Kwankwaso-
Rabiu-Musa-Kwankwaso-

Tsohon ministan tsaron Nigeria, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce kamata yayi rundunar yan sandan Kano, ta rika nuna kwarewa a ayyukanta, da kuma gujewa furta kalaman da zasu zama barazana ga mutane.

Kalaman Kwankwaso, sun kasance wani martani ne daya aikewa rundunar akan yadda ta sanar da cewa wasu yan ta’adda na shirin kai harin ta’addanci jihar Kano, kafin gudanar da Maulidin Tijjaniyya na kasa daya gudana ranar asabar a filin wasa na Sani Abacha, dake Kofar Mata.

:::An kori jami’an EFCC 27 daga aiki saboda aikata laifin cin hanci da rashawa

Sai dai duk da barazanar da yan sandan suka nuna an gudanar da taron maulidin cikin kwanciyar hankali, ba tare da ko jikkata mutum guda ba.

Kwankwaso yayi amfani da wannan dama wajen mika sakon kammala taron lafiya ga gwamnan jihar Kano, da Sarkin Kano, har ma da mabiya darikar Tijjaniyya, bisa yadda aka yi taron cikin lumana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here