Wasu bata gari da ake kyautata zaton yan ta’adda ne sun kai hari yankin Chikakore, dake Kubwa, a karamar hukumar Bwari, ta birnin tarayya Abuja, inda suka sace wani mutum da matar sa, sai dansa da wasu karin mutane 2.
:::Ya kamata yan sandan Kano su rika nuna kwarewa a aikin su—Kwankwaso
Mazauna yankin da abin ya faru sun shaidawa Daily Trust, cewa yan ta’addan da suka sace mutanen sun kai yawan mmutum 30, dauke da manyan makamai da tsakar daren litinin, tare da tafiya kai tsaye zuwa gidan wani mai suna Adefija Micheal, wanda shi aka sace tare da iyalansa.
Majiyar ta kara da cewa maharan sun kuma kai hari wani gini na gidan gona wanda a nan ma suka jikkata wani mutu tare da sace matar sa.
Kawo yanzu ba’a samu martanin rundunar yan sandan Abuja kan lamarin ba, saboda an kira mai magana da yawun rundunar Josephine Adeh, inda tace tana yin tukin mota zuwa wajen aiki amma zata yi karin haske in ta isa ofishi, sai dai kawo lokacin rubuta wannnan labari, bata kira wayar ba.