Ma’aikatar tsaro ta ja kunnen Rotimi Ameachi

0
59

Karamin ministan tsaro Bello Matawalle, ya kalubalanci kalaman tsohon ministan sufuri Rotimi Ameachi, da ya nemi matasa su nemar wa kansu yanci a yanayin kuncin rayuwa da ake fama da shi.

Matawalle, ya zargi Ameachi, da yunkurin tayar da tarzoma a kasar nan.

A makon da muke ciki ne Rotimi Ameachi, yace matasan Nigeria suna cikin halin kuncin rayuwa kuma sun kasa nema wa kansu mafita, ko da ta hanyar yin zanga zanga ce.

Karanta karin wasu labaran:Ministan tsaro ya nemi yan ta’adda su ajiye makaman su ko a kashe su

A cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar tsaro Henshaw Ogubike, ya fitar a yau, Matawalle ya gargadi Ameachi da ya dakata da yin kalaman tunzura al’umma.

A cewar ministan, shugaban Nigeria yana kan aikin lalubo bakin zaren magance kalubalen da kasar ke ciki.

Karin farashin man fetur da tsadar rayuwa na daga cikin dalilan Ameachi, na neman yan Nigeria su nemar wa kansu mafita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here