Ministan tsaro ya nemi yan ta’adda su ajiye makaman su ko a kashe su

0
155

Karamin ministan tsaro Bello Matawalle, ya gargadi yan fashin daji da sauran yan ta’addan kasar nan su gaggauta ajiye makaman su ko kuma jami’an tsaro su mayar da su zuwa ga mahaliccin su.

Yace in har masu tayar da hankalin al’umma basu rungumi zaman lafiya ba, tabbas zasu rasa rayuwar su.

Matawalle, ya bayyana hakan a yau lokacin da yaje ziyarar aiki kauyen Gundumi, dake karamar hukumar Sabon Birni dake Sokoto.

Karanta karin wasu labaran:Akwai bukatar dauko hayar jami’an tsaro a Nigeria——NDUME

Ministan ya nuna takaicin sa akan yadda ya tarar da mutane kadan ne suke rayuwa a garin tare da cewa kamata yayi garin ya kasance cikin harkokin kasuwanci da walwalar jama’a.

Sai dai yace nan bada jimawa komai zai daidaita, sannan za’a kafa sansanin sojoji a kauyen na Gundumi.

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, ya ce dole ne mutane suji tsoron Allah, su daina bawa yan ta’adda bayanai akan yan uwan su ko jami’an tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here