Gwamnatin tarayya tace babu hannun ta a karin farashin man fetur

0
128

Gwamnatin tarayya tace babu hannun ta a karin farashin man fetur da kamfanin NNPCL yayi a jiya laraba.

Farashin ya tashi a gidajen man NNPCL daga 897, zuwa 1030, a Abuja yayin da yakai 1070, a wasu jihohin, sannan farashin bashi da tabbas a gidajen man yan kasuwa, sakamakon cewa akwai inda ake siyarwa 1150, wani wajen fiye da haka.

Karin ya haifar da bayyana mabanbantan ra’ayoyi daga yan Nigeria masu bukatar Tinubu ya yi gaggawar dawo da farashin man da aka sani a baya.

Karanta karin wasu labaran:NNPCL ya bawa Matatar Dangote gangar mai miliyan 48

A zantawa da jaridar Daily Trust, tayi da ministan yada labarai Mohammed Idris, yace gwamnatin tarayya bata da hannu a karin farashin, Kuma ba ita za’a dorawa laifi akan hakan ba.

Yace kamfanin NNPCL ya kara farashin ne bayan samun canji daga fannin makamashi, inda yace NNPCL bai nemi shawara ko umarnin gwamnati akan karin farashin ba, saboda gwamnatin bata da damar karawa ko rage farashin man, in aka yi la’akari da dokar fannin mai da tsohon shugaban kasa Buhari, ya sakawa hannu a lokacin mulkin sa mai suna PIA.

Mohammed Idris, ya ce akwai bukatar yan Nigeria su rika fahimtar kamfanin NNPCL da gwamnati inda a cewar sa nan gaba farashin man zai yi kasa.

Sannan yace kudaden da ake tarawa na tallafin man da aka cire za’a yi amfani da su a fannin ilimi, lafiya, tsaro da sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here