Kotu ta daure dan kasar Lebanon mai yin lalata da yara a Kano

0
77

Wata babbar kotun tarayya da ke birnin Kano, ta yanke wa wani dan kasar Lebanon mai suna Zuhier R Akar mai shekaru 67 hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari bisa samunsa da laifin lalata da wasu ‘yan mata biyu.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP) reshen jihar Kano, ta gurfanar da Akar mazaunin Gidan Wanka, dake unguwar Unity Road, a karamar hukumar Fagge, da laifuka biyu na safarar mutane da kuma lalata da su.

Da yake yanke hukunci, Mai shari’a SM Shu’aibu, ya bayyana cewa masu gabatar da kara sun tabbatarwa da kotu shaidun da take bukata ba tare da wata matsala ba.

Karanta karin wasu labaran:Kungiyoyin APC zasu kai Ganduje kara gaban kotu

Shu’aibu ya yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba.

Tun da farko, lauyan masu gabatar da kara kuma kwamandan NAPTIP shiyyar Kano Abdullahi Babale, ya shaida wa kotun cewa hukumar tsaron farin kaya (DSS) dake Kano, ta kai rahoton lamarin ga hukumar sa a ranar 5 ga Satumba, 2024.

Babale ya ce wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 4 ga watan Satumba da misalin karfe 10:30 na dare a gidansa da ke Gidan Wanka, Unity Road Kano.

Wanda ake tuhumar ya yi safarar ‘yan matan masu shekaru 14 da 15 daga Titin Civic Centre, sannan ya kai su gidansa ya yi lalata da su.

Tun da farko wanda ake tuhumar ya amsa laifin da ake tuhumar sa.

Laifin ya ci karo da tanadin sashe na 16(1) na dokar hana fataucin mutane.

Lauyan wanda ake kara, R A Kasali, ya roki a yiwa wanda yake karewa sassauci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here