Wani matashi mai suna Yusuf ya rasa ransa bayan wani rikici da ya barke a harabar Kamfanin Mamuda Group da ke Challawa, Kano, abin da ke cigaba da tayar da kura a kafafen sada zumunta.
Bayanan farko da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna cewa rikicin ya faru ne tsakanin Yusuf da wani ma’aikaci a kamfanin, wanda aka ce ya daba masa wuka. Wasu rahotanni na cewa Yusuf ya koma kamfanin domin karɓar hakkinsa bayan sallama daga aiki, kafin rikicin ya barke.
Iyalan mamacin sun bukaci hukuma ta dauki mataki.
A wata hira da mahaifiyar Yusuf ta yi da Freedom Radio Kano, ta bayyana cewa rikicin ba sabon abu ba ne, kasancewar marigayin da wanda ake zargi sun dade suna sabani.
Martanin Kamfanin Mamuda Group:
Jami’in hulda da jama’a na kamfanin, Bashir Alhasan Indabawa, ya musanta rahotannin da ke cewa wani babban jami’in kamfanin ne ya daba masa wuka. Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne tsakanin wasu ma’aikata biyu ne a wajen harabar kamfanin, kuma dukansu kananan ma’aikata ne.
Ya kara da cewa kamfanin na da bidiyo na abin da ya faru, kuma yana da hujja cewa ma’aikatan sun nemi izinin fita daga wajen aiki a lokacin da lamarin ya auku. Har ila yau, ya bayyana cewa kamfanin ne da kansa ya kai wanda aka jikkata asibiti tare da hadin gwiwar ‘yan sanda, kafin daga bisani ya rasu.
Hukuma na ci gaba da bincike
Yayin da ake cigaba da jiran cikakken bayani daga rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro, jama’a a kafafen sada zumunta na cigaba da bayyana ra’ayoyinsu kan lamarin, suna bukatar a tabbatar da adalci ga mamacin da iyalansa.