Hadakar jam’iyyu ba zata bawa Tinubu matsala ba—Gwamnan Kaduna

0
7
Uba Sani

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa shirin kafa wata jam’iyyar haɗaka da ake yi ba wata barazana ba ce ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ba ko APC.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani shirin siyasa da ake gabatarwa a Channels Television mai suna Politics Today, a ranar Juma’a.

“Zan faɗa muku, ku rubuta, babu wata barazana da Tinubu ke fuskanta,” in ji Gwamna Uba Sani.

Ya bayyana haka ne yana mai mayar da martani kan ƙaddamar da wata ƙungiya mai suna National Opposition Coalition Group, wadda tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark, ke jagoranta.

A cewarsa, mafi yawan waɗanda ke mara wa haɗakar baya ba su da cikakken tarihi ko fahimta game da yadda masu fafutuka suka sha wahala wajen tabbatar da dimokuraɗiyya da shugabanci nagari a Najeriya.

“Mutanen da ke ta magana a yau, ina suke lokacin da ake gwagwarmayar tabbatar da dimokuraɗiyya, adalci, da mulki na gaskiya a wannan ƙasa? Ba su da masaniya a kai,” in ji gwamnan.

Gwamna Uba Sani ya ƙara da cewa baya jin tsoron tasirin jam’iyyun adawa a jihar Kaduna, ganin irin kokarin da gwamnatinsa ke ci gaba da yi wajen kawo cigaba da inganta rayuwar al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here