Fashewar Bam ta kashe mutane 5 a jihar Kano
Aƙalla mutum biyar ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu goma 10 suka jikkata sakamakon fashewar wani bam da ta auku a Jihar Kano, a yau Asabar.
Fashewar ta haddasa firgici da rudani a yankin da lamarin ya faru, lamarin da ya sa jami’an tsaro da na agajin gaggawa suka garzaya wurin domin ceto rayuka da bada taimako.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa alamun farko na nuna cewa wani bam ne da ake zargin na sojoji ne, wanda wata babbar mota ke ɗauke da shi, ya fashe yayin jigilar sa.
“Na samu kiran gaggawa cewa wani abu mai tayar da hankali ya faru. Da na isa wajen, sai na ga abin kamar bama-baman da ake amfani da su ne wajen atisayen sojoji suka fashe. Mutum 15 sun jikkata, kuma abin takaici, guda biyar sun rigamu gidan gaskiya,” in ji Kwamishinan.
Kwamishinan ya ce an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitocin da ke kusa domin samun kulawa ta gaggawa.
Ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna cewa wata babbar mota ce ke ɗauke da kayan fashewa, wadda ake zargin tana kan hanyar zuwa Jihar Yobe kafin lamarin ya faru.
Sai dai har yanzu, ba a tabbatar da ko motar sojoji ce ke ɗauke da kayan ba, kuma hukumomi na ci gaba da gudanar da bincike domin gano hakikanin musabbabin fashewar.
“Za mu fitar da cikakken bayani bayan kammala bincike,” in ji Kwamishinan.
Ya kuma roƙi al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da bai wa hukumomi hadin kai domin samun bayani akan gaskiyar lamarin daya faru.