Fitaccen Jarumin Kannywood, Abdurrazak Sultan, ya kamu da rashin lafiya bayan kammala aikin hajji

0
58

Fitaccen jarumin fina-finan Kannywood kuma sananne wajen fassara fina-finan Indiya, Abdurrazak Sultan, ya kamu da rashin lafiya bayan kammala aikin Hajjin bana a ƙasar Saudiyya.

Sultan ya tafi aikin Hajji ne kwanaki kaɗan bayan ɗaura auren sa da amaryarsa Amina. Abokinsa, Abdussamad Ishaq, ne ya bayyana wannan labari ta shafinsa na Facebook, inda ya roƙi al’umma su sanya jarumin a cikin addu’o’insu.

Sai dai har yanzu ba a bayyana irin ciwon da ke damunsa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here