Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana goyon bayan sa ga matakin da Shugaban ƙasa Tinubu ya dauka na ayyana dokar ta ɓaci a jihar Ribas.
Wike yace burin sa shine a cire Fubara daga mulkin Rivers ba wai dakatarwa ba.
Idan za’a iya tunawa Tinubu ya ɗauki matakin dakatar da gwamna Siminalaya Fubara da mataimakiyar sa da ƴan majalisar dokokin jihar biyo bayan rikicin siyasar daya dabaibaye jihar.
Amma Wike ya ce matakin da shugaban kasar ya dauka ne ya ceto Ribas daga rushewa, yana mai cewa shawarar da aka yanke ta naɗa shugaban rikon kwarya bayan dakatar da Fubara mataki ne da ya dace.
Tsohon gwamnan na jihar Ribas Nyesom Wike ya bayyana hakan ne a yai Juma’a a birnin tarayya Abuja yayin wata tattaunawa da ‘yan jarida.