Ana kyautata zaton mayaƙan Boko Haram sun kai hari a sabuwar unguwar Yamtake da ke Ƙaramar hukumar Gwoza a Jihar Borno.
Mayaƙan sun kashe sojoji biyu tare da wasu fararen hula da ba a bayyana adadinsu ba.
Majiyoyin tsaro da na cikin gida sun tabbatar da harin, inda suka ce maharan sun mamaye unguwar da misalin ƙarfe 11:15 na daren Alhamis.
Ɗaya daga cikin majiyar ta ce, kafin a aike da wata tawagar sojoji daga Gwoza, maharan sun riga sun afkawa jama’a da sansanin sojojin Yamtake.