Ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, yace jam’iyyar PDP bata shiryawa karɓar mulki a hannun APC ba a kakar zaɓe ta shekarar 2027.
A cewar Wike ko kaɗan babu wani cikakken tsarin da PDP ta yi wanda ke nuna cewa tana da shirin karɓar mulkin.
Ministan ya bayyana hakan a yau juma’a lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Nyesom Wike, dai na daga cikin manyan ƙusoshin gwamnatin tarayya wanda har yanzu ke yin ikirarin cewa shi ɗan jam’iyyar PDP ne, tare da shan alwashin yin duk mai yiwuwa wajen kayar da ita a zabe mai zuwa.