Shugaban kasa Bola Tinubu, ya nemi hukumomin dake kare hadura dasu kawo mafita dangane da yadda fashewar tankokin dakon man fetur ke hallaka mutane basu kakkautawa.
Tuni dai shugaban ya umarci hukumar dake kare afkuwar hadura ta Nigeria FRSC, da sauran hukumomin dake da alhakin kula da hanyoyi su kawo tsarin da zai yi maganin hatsarin fashewar tankunan fetur da hakan ya yi sanadiyyar rayukan mutane a jihohin Niger da Enugu, a wannan wata da muke ciki.
:::Yan ta’adda sun sace mutane a birnin tarayya Abuja
A lahadin zata gabata ne fashewar tankar tayi sanadin mutuwar mutun 18, a Enugu, kwanaki kadan bayan irin hakan ya faru a jihar Niger da mutane fiye da 90, suka rasu, bayan fashewar data hallaka mutane fiye da 200, a jihar Jigawa.
Tuni dai shugaban kasar ya mika sakon ta’aziyyar sa ga iyalan wadanda suka rasu sanadiyyar fashewar tankar Enugu, da kuma jajantawa wadanda suka yi asara.
Tukin ganganci da rashin rashin kyawun hanya na daga cikin manyan dalilan dake haddasa hatsarin tankokin man.