Malaman Kano sun yi kira da a zabi Atiku don tabbatar da hadin kan Najeriya

0
99

Kungiyar malaman addinin musulunci a Kano ta bayyana goyon bayanta ga dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar bisa goyon bayan tikitin musulmi da kirista sabanin tikitin musulmi da musulmi na jam’iyyar APC mai mulki.

Shugaban kungiyar Sheikh Adam Koki ya shaidawa manema labarai hakan jim kadan bayan fitowa daga wani taro da aka yi a Kano a ranar Laraba, cewa sun gamsu da yadda Atiku ke mutunta kasa mai addini daban-daban.

Malamin ya bayyana cewa,  hadin kai a tsakanin ‘yan kasa yana da matukar tasiri ga cigaban kasa, amma mayar da wani bangare na kasar saniyar ware kamar cin amana ne.

Ya ce sun yi wa dukkan ’yan takarar kallo da idon basira, inda suka cimma matsaya kan cewa Atiku ba wai ya cancanta a jiki kadai ba, har ma ya fi kowa kwarewa da zai iya fitar da Nijeriya daga cikin kangin halin da ta tsinci kanta, kasancewar ya taba zama mataimakin shugaban kasa a baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here