Yadda canjin kudi ya gurgunta ayyukan ’yan ta’adda – Rundunar soji

0
96

Kwamdan rundunar hadin gwiwa mai yaki da ta’addanci a shiyyar Arewa maso Gabas, Manjo-Janar Ibrahim Salihu Ali, ya ce matakin sauya fasalin Naira da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya dauka ya taimaka wajen kassara ayyukan ’yan ta’adda a shiyar.

Ali ya  bayyana haka ne a ganawarsu da ’yan jarida ranar Talata a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Game da batun canjin kudi, Ali ya ce “Mataki ne mai kyau, zai taimaka kuma a zahiri  matakin ya takaita wajen rage matsalar garkuwa da mutane.

“Ta bangaren ’yan bindiga kuwa, abin da muke gani yanzu shi ne suna kama mutane sannan su bukaci a ba su kudi da abinci saboda ba su da zarafin amfani da wadannan abubuwa.

“Don haka mataki ne mai kyau, mataki ne da ya kamata ya dore,” in ji shi.

Jami’in ya ce suna sane da wani bidiyo na ’yan bindiga da aka yada a kafafen sada zumunta da ke nuna barazanar kai wa jama’a a ranar zabe, kuma za su dakile hakan.

Ya kara da cewa, akwai yiwuwar ganin irin wannan bidiyon da zarar babban al’amari na shirin aukuwa a kasa kamar zabe da sauransu.

A karshen taron, shugaban Kungiyar ’Yan Jarida ta Kasa (NUJ) reshen jihar, Dauda Illiya, ya nuna godiya bisa yadda rundunar soja take aiki tare da ’yan jarida a jihar da ma kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here