DSS ta tsananta binciken Emefiele kan daukar nauyin ta’addanci

0
98

Hukumar tsaro ta DSS ta tsananta bincike a kan gwmanan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, domin gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin almundahana da kuma daukar nauyin kungiyar ta’addanci ta IPOB.

DSS tana kuma zargin Mista Emefiele da damfara da kuma amfani da shirye-shiryen tallafin CBN wajen azurta kansa, karkatar da kudaden gwamnati da kuma yi mata zagon kasa.

Aminiya ta gano haka ne a yayin da wasu rahotanni ke zargin rundunar Sojin Kasa ta Najeriya da bai wa Emefiele kariya a gida da kuma ofishinsa, domin hana a kama shi, zargin da hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta musanta.

Bayan yunkurin DSS na tsare gwamnan CBN din a baya ya faskara, hukumar ta bi wasu sabbin hanyoyi tare da tsananta bincike a kansa kan zage-zagen da ake masa.

A baya-bayan nan kafar yada labarai ta Premium Times ta wallafa wasu bayanai na musamman da ta samu daga kotu kan zarge-zargen da Emefiele ke fuskanta.

Takardar kotun ta nuna ana zargin gwmanan CBN din da daukar nauyin ’yan bindiga da kuma ayyukan kungiyar ta’addanci ta IPOB.

Rahoton ya kuma zargi Emefiele da yin zagon kasa ga gwamnatin shugaba Buhari, daukar nauyin ta’addanci da kuma wasu abubuwa da ke barazana ga tsaron Najeriya.

Ana kuma zargin sa da facaka da kudaden Bankin NIRSAL da kuma kudaden shirin tallafin noma na Anchor Borrower wadanda CBN ke kula da su.

Ana zargin gwmanan na CBN ne da daukar nauyin reshen soji na kungiyar IPOB, wato ESN, ta hanyar amfani da kudaden sata da kuma wadanda ya yi amfani da su wajen neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki, wanda Bola Tinubu ya lashe zaben fidda gwanin.

Gwamnatin Tarayya ta jima da ayyana IPOB a matsayin Kungiyar ta’addanci.

IPOB dai kungiya ce da ke neman ballewa daga Najeriya, kuma ta dade tana kai miyagun hare-hare a kan cibiyoyin gwamnati da na hukumomin tsaro tare da kashe mutane, musamman jami’an tsaro.

Maharan IPOB sun kuma kashe fararen hula da dama, tare da tilasta wa mazauna yankunan Kudu maso gabashin Najeriya zaman gida a ranakun litinin.

baya-bayan nan dai IPOB ta tsananta kai hare-hare a kan ofisoshin ’yan sanda, inda take kashe jami’ai ta sace makamai, sai kuma ofisoshin hukumar zabe ta Kasa (INEC), inda suke kona kayayyakin zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here