’Yan sanda sun kama ’yan fashi da dillalin kwaya a Jigawa

0
98

’Yan sanda sun cafke wasu mutum biyu da ake zargin ’yan fashi da makami ne da wani dillalan miyagun kwayoyi a kananan hukumomin Kaugama da Taura a Jihar Jigawa.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu ne, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a a ranar Litinin cewa hadin gwiwar ’yan sanda, mafarauta da ’yan banga sun kama su ne ne bayan sun tare hanya sun yi wa ’yan kasuwar da ke dawowa daga kasuwar Gujungu ta mako-mako fashi a tsakanin kauyukan Marke da Sundum a Karamar Hukumar Kaugama.

Shiisu ya ce wadanda ake zargin, masu shekaru 20 da 22 mazauna kauyen Marke ne kuma sun amsa cewar sun tare hanya tare da aikata fashi da makami.

Ya ce rundunar ta kai samame a yankin Taura Bakin Rafi da ke yankin inda kama wani dillalin miyagun kwayoyi mai shekara 25, mazaunin Malamawar Taura, dauke da kullin kwaya guda 50, wiwi guda 40.

A cewarsa, Kwamishinan ’yan sandan jihar, Emmanuel Ekot ya yaba da kokarin jami’an tare da bayar da umarnin gudanar da bincike da kama damko sauran wadanda ake zargi da karbar kayan da aka sace.

Ekot ta bukaci al’ummar jihar masu son zaman lafiya da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai ga ’yan sanda don taimakawa wajen dakile miyagun laifuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here