An dawo da ‘yan Najeriya 150 daga jamhuriyar Nijar

0
121

Gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar kungiyar kula da ‘yan cirani ta duniya (IOM) da kungiyar ECOWAS, sun dawo da ‘yan Najeriya 150 da suka makale daga (Niamey) Jamhuriyar Nijar.

Ministar jin kai, da kula da bala’o’i da ci gaban jama’a, Sadiya Umar-Farouq, ce ta bayyana hakan yayin da take karbar mutanen da suka dawo a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke Kano a ranar litinin.

Umar-Farouq wanda Daraktan Agaji na Ma’aikatar Grema Ali ya wakilta ta ce wadanda suka dawo sun isa filin jirgin ne da misalin karfe 3:45 na rana.

Jirgin saman SKY MALI ne ya yi jigilar wadanda suka dawo zuwa Najeriya, wanda masana’antar sufurin jiragen sama na Habasha tai jigilar su.
A cewarta, an mayar da mutanen gida Najeriya ne ta hanyar wani shiri da suka bullo dashi.

“Shirin an yi shi ne ga ‘yan Najeriya da ke cikin mawuyacin hali da suka bar kasar don neman wuraren aiki a fadin kasashen Turai da Afirka amma ba su iya komawa lokacin da tafiyar tasu ta samu tasgaro,” inji shi.

Wadanda aka dawo da su sun hada da maza 125, mata 14 da yara 11.

“Wadanda aka dawo da su sun fito ne daga sassa daban-daban na Najeriya musamman Yobe, Kaduna, Bauchi, Sokoto, Katsina da Kano da sauransu,” inji ta.

Ta yi bayanin cewa wadanda suka dawo za su yi horo na kwanaki uku kan yadda za su samu dorewar kansu sannan za a ba su jari domin su samu damar yin sana’o’i masu inganci don dogaro da kai.

Ta kuma shawarci jama’a da su guji jefa rayuwarsu cikin hadari ta hanyar tafiye-tafiyen neman wuraren aiki a wasu kasashen, ta kara da cewa babu wata kasa da ta fi kasarsu ta asali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here