An kashe ‘yan bindiga 3 lokacin da suka kai hari ofishin ‘yan sanda da ke Anambra

0
115

Wasu gungun ‘yan banga sun bindige wasu ‘yan bindiga uku a wani yunkurin kai hari a ofishin ‘yan sanda da ke jihar Anambra.

LEADERSHIP ta samu labarin cewa an kashe ‘yan bindigar ne a safiyar ranar Litinin a lokacin da suka yi yunkurin kai hari ofishin ‘yan sanda na Awada da ke kusa da garin Obosi a karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar.

Yayin da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), DSP Ikenga Tochukwu, har yanzun bai ce uffan ba dangane da lamarin, har zuwa lokacin hada wannan rahoton, sakataren yada labarai na gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, Mista Christian Aburime, ya tabbatar da afkuwar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here