NIS ta sauyawa wasu manyan jami’anta jihohi gabanin zaben 2023

0
100

Kwanturolan hukumar shige da fice na kasa, Isah Jere Idris, ya amince da a sauyawa wasu manyan hafsoshi 41 jihohin da suke aiki gabanin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da za a gudanar mako mai zuwa.

A wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na NIS, Tony Akuneme, ya sanyawa hannu, ya ce sabon sauyin wuraren aikin ya shafi mataimakan Kwanturola Janar na shiyyoyi daban-daban da kuma Kwanturola talatin da aka tura zuwa sabbin jihohi.

A cewar sanarwar, wacce mataimakin Kwanturolan Janar Usman Babangida ya sanya wa hannu, ya ce jihohin da abin ya shafa sun fi shafar iyakar Nijeriya da kasashe makwabta, kamar Yobe, Adamawa, Sokoto, Katsina, Zamfara da Oyo da Lagos (Seme Border) da kuma Cross River.

Sauran jihohin sun hada da Gombe, Kaduna, Kano, Plateau, Bauchi, FCT, Nassarawa, Edo, Bayelsa, Ribas, Anambra da Enugu, da dai sauransu.

Kakakin NIS ya ci gaba da cewa, Jami’an da sauyin ya shafa za su fara aikin na nan take, kuma hukumar ta CGIS ta ba da wani kaso mai tsoka kan rawar da jami’an sa za su taka wajen samun nasarar babban zabe mai zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here