Idan ta kama za mu katse hutunmu don samar wa ‘yan Najeriya mafita a kan batun sauyin kudi – Sanata Uba Sani

0
126

Yayin da ake ci gaba da kiki-kaka tsakanin bangaren zartarwa da wasu gwamnatocin jihohi a Najeriya game da batun sauyin kudi, ‘yan majalisar dattawan kasar sun ce za su iya katse hutun da suke yi idan ta kama domin su samar wa al’ummar kasar mafita.

‘Yan majalisar dattawan sun bayyana hakan ne bayan da shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya umarci babban bankin kasar ya fitar da tsoffin takardun naira dari biyu domin a ci gaba da hada-hada da su sakamakon karancin da ake fuskanta na sabon kudi, duk kuwa da cewa kotu ta umarci gwamnati ta saurara.

Sanata Uba Sani, shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawan da ke kula da harkar banki, ya shaida wa BBC cewa ya kamata bangarorin gwamnati su dinga martaba juna ta yadda dimokradiyya za ta bunkasa.

Ya ce, “Kamar yadda shugaban kasa ya yi jawabi cewa yana so a ci gaba da amfani da tsohon kudi na naira 200, to a bangarenmu na majalisar dattawa muna ganin wannan mataki na da matukar hadari.”

Dan majalisar dattawan, ya ce idan ana so dimokradiyya ta dore da kuma bunkasa, to ya kamata matakan gwamnati ukun nan wato da na zartarwa da na shari’a da kuma su bangaren majalisar dokokin su rinka biyayya ga dukkan wani hukunci na kotun koli.

Ya ce, “Rashin bin umarnin kotun babbar barazana ce ga dimokradiyya.”

Sanata Uba Sani, ya ce sun san shugaban kasa na da hurumin amfani da dokokin kasa, to amma idan har kotu ta ce ga abin da ya kamata a yi, ya kamata abi umarnin kotun.

Ya ce, “A halin da ake ciki a kasar nan ya kamata kowa ya saurara ya ji hukuncin da kotun za ta yanke a kan batun wa’adin amfani da tsoffin takardun kudi.”

Dan majalisar dattawan ya ce su abin da ke damunsu shi ne wannan matakin da sauya fasalin kudi da kuma wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kudi ba wanda yafi shafa yake shan wahala irin talaka.

Ya ce, “Binciken da muka yi ya nuna yadda ‘yan kasuwa ke karya farashin kayayyakinsu suke samun biyan bukata, don haka ni a ganina wannan abu da aka yi karya tattalin arzikin talakan Najeriya ne.”

Sanata Uba Sani, ya ce, “Idan har al’amura suka ci gaba a haka bayan kotun koli ta yanke hukunci, idan har ba a samu matsaya ba, to mu ‘yan majalisa dole mu koma cikin gaggawa saboda muna da dokar da ta bamu damar mu dauki matakai masu karfi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here