Mutane 20 sun mutu a wata taho-mu-gama tsakanin motar Soji da bas

0
102

Akalla mutane 20 ne suka mutu yayinda wasu 60 suka jikkata a wata taho mu gama da aka yi tsakanin motar fasinja kirar bas da wata motar soji mai sulke a Afrika ta Kudu. 

Rahotanni sun bayyana cewa hadarin ya faru ne da misalin karfe 3 na rana agogon GMT a ranar Litinin ddata gabata a Limpopo, wani lardi da ke yankin arewa mai nisa na kasar, a kan iyakarta da Zimbabwe.

A wata sanarwa, ma’aikatar sufurin kasar ta ce mutrane 20 ne suka mutu a cikin wani yanayi mai tayar da hankali, bayan da mota mai sulke din ta kwace wa direbanta, ta kuma yi karo da motar bas da ke tahowa.

Har yanzu ba a tantance musabbabin wannan hatsari ba, sai dai mai magana yawun ma’aikatar sufuri, Tidimalo Chuene sun ce a ilahirin daren da ya gabaci ranar, an yi ta zabga ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Larduna da dama na Afrika ta Kudu sun  fuskanci ruwan sama kamar da bakin kwarya na tsawon kwanaki, lamarin da ya haddasa ambaliyar ruwa, wadda taa yi sanadin mutuwar mutane 7, kana da  dama suka bace bat.

Cibiyar hasashen yannayi taa kasar ta yi has ashen za a ci gaba da zabga ruwan sama a sassan kasar na tsawon kwanaki, tana mai kashedin cewa ana iya samun karin ambaliya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here