Kotu ta sabunta umarnin hana PDP korar gwamna Wike

0
119

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja karkashin jagorancin mai shari’a John Kayode Omotosho, ta sabunta umarnin da ta bayar a ranar 2 ga watan Fabrairu, inda ta haramta wa jam’iyyar PDP da shugabanninta daukar matakin korar gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, daga mukaminsa. Kotun ta sabunta umarnin a ci gaba da sauraron karar mai lamba: FHC/ABJ/CS/139/2023 da Gwamna Wike ya shigar.

Gwamnan yana kalubalantar jam’iyyar da sauran shugabannimta, dacewar barazanar da ake zargin shugabannin jam’iyyar PDP na dakatar da shi ko kuma su kore shi. Wadanda ake tuhuma a karar sun hada da PDP; Kwamitin Ayyuka na kasa (NWC) na PDP; Majalisar Zartarwa ta kasa (NEC) ta PDP; Dr. Iyiochia Ayu; sakataren kasa, Samuel Anyanwu, da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here