DA DUMI-DUMI: ‘Yan sanda sun kama wani Fasto a Abuja da laifin yin wa’azi dauke da AK-47

0
117

Rundunar ‘yan sanda ta tsare shugaban limaman cocin House on The Rock da ke Abuja, Fasto Uche Aigbe, bisa laifin daukar AK-47 zuwa kan mimbarin wa’azi.

Tawagar ta Intelligence Response Team, IRT, karkashin hukumar leken asiri ta Force Intelligence Bureau, FIB, ta kama Aigbe.

‘Yan sandan sun fara gudanar da bincike ne bayan wani faifan bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta.

Ana ganin malamin yana wa’azi a coci ranar Lahadi yayin da yake dauke da bindiga a kafadarsa ta hagu.

Jaridar daily news24 Hausa ta rawaito cewa wani Insfekta Musa Audu ne ya bawa Aigbe bindigar aikin sa wanda ya je da’ita cocin yayin wa’azi.

A cewar hukumar yan sanda Jami’in zai fuskanci hukunci dai dai da abinda ya shuka.

Kwamishinan ‘yan sanda reshen babban birnin tarayya, Sadiq Abubakar ya bukaci a kori  Audu daga aiki saboda rashin da’a.

CP ya ba da shawara ga Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba.

Ana sa ran hukumar tsaro za ta bayar da cikakken bayani kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here