Mai jego ta rataye kanta a Borno

0
221

Ana fargabar wata matar aure mai ’ya’ya tara ta rataye kanta ta bar jariri mai wata hudu a duniya a Jihar Borno.

Gab da Magaribar ranar Asabar ce aka tsinci gawar mai jegon a rataye a cikin gida ta bar jaririn nata a gefe, a unguwar Sajeri da ke gundumar Gumari a Karamar Hukumar Jere ta jihar.

Wani ganau, Baa Modu, ya ce mijin matar da ’ya’yan ba sa gida a lokacin da abin ya faru, ’ya’yan ne suka fara dawowa suka iske gawarta a rataye a cikin gida.

Baa Modua ya ce, ’ya’yan ne suka fito suka sanar da jama’a abin da suka gani, “Da muka shiga mun samu babban dan ya samu ya yanke igiyar, gawar tana kwance a kasa, a gefen ta kuma ga jaririnta mai wata hudu.”

Ya ce ba a samu wata takarda da ke nuna dalilin abin da ake zargin ta aikata ba.

Amma wani ganau kuma makusancin iyalin ya ce matakin da ake zargin matar ta dauka, wuce gona da iri ne, saboda rashin jin dadinta kan sauya gidansu da suka yi.

Ya ce, “Danta ya bayyana cewa ba ta so dawowarsu gidan na ba, bayan da aka tashe su daga tsohon gidansu da ke Bulunkutu Kasuwa.

“Don ta nuna bacin rantam sai ta kwashe kayanta ta koma gidan iyayenta; sai jiya aka dawo da ita, ba wanda ya san abin da zai biyo baya ke nan.”

Kokarin wakilinmu na samun mijin matar ko jin ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar Borno, Muhammad Shatambaya, kan wannan lamari dai bai yi nasara ba.

Domin kuwa har muka kammala haɗa wannan rahoton, kakakin’yan sandan bai amsa kiran waya ba.

Shi kuma mijin, ya tafi kai wa ’yan sanda rahoto, amma bai dawo ba, kuma ba a same shi a waya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here