Canjin kudi ya rage satar mutane da karbar rashawa —Malami

0
123

Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya bayyana cewa canjin kudi ta Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi ya taimaka wajen rage aikata ayyukan garkuwa da mutane.

Malami, ya bayyana haka ne cikin wata hira da ya yi da Gidan Rediyon Tarayya da ke Kaduna, inda ya ce jama’a ba sa ganin nasara da tsarin ya haifar.

Malami, ya bayyana haka ne cikin wata hira da ya yi da Gidan Rediyon Tarayya da ke Kaduna, inda ya ce jama’a ba sa ganin nasara da tsarin ya haifar.

Da yake bayyana hakan a ranar Juma’a, Malami ya ce: “Na fada muku maganar tana gaban kotu, ba za mu bijire wa kotu ba, za mu bi umarnin kotu amma muna da ’yancin fada wa kotu alfanun da tsarin ya haifar.

“Idan ba ku ga amfanin tsarin ba, ya kamata kuma a gefe daya ku ga alfanunsa.

“Idan wadancan gwamnonin sun bayyana wa kotu wahalar da ake sha saboda tsarin, ya kamata kuma a fahimci cewa tsarin a gefe daya yana warware wasu matsalolin.

“Na ba ku misali da matsalar tsaro; Tun bayan da aka kaddamar da wannan tsarin garkuwa da mutane ya ragu.

“Sannan ya rage yawan cin hanci da rashawa, don haka muna da ’yancin zuwa mu bayyana wa kotu amfanin da tsarin ya haifar.

“Kotun ta yanke hukunci ba tare da sauraron bangaren gwamnati ba, amma ta sanya 15 ga Fabrairu a matsayin ranar da za ta saurari tsagin gwamnati.

“Kowa ya san dalilin da aka zabi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, saboda ya yaki cin hanci da matsalar tsaro ya kuma bunkasa tattalin arziki. Don haka za mu bukaci kotu ta kalli kowane bangare.”

Idan ba a manta ba a satin da ya wuce ne gwamnatocin jihohin Kaduna, Zamfara da Kogi suka maka Gwamnatin Tarayya a Kotun Koli inda suka bukaci kotun da dakatar da hana amfani da tsofaffin takardun kudi.

Wannan dai na zuwa ne bayan wahala da talakawa suka shiga sakamakon canjin kudi da CBN ya yi, wanda hakan ya sa kasuwancin wasu ke neman durkushewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here