An gurfanar da matar gwamnan Kogi a gaban kotu kan badakalar biliyan 3

0
113

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ta gurfanar da Rashida Bello, matar Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, a gaban kotu bisa zargin almundahana.

An gurfanar da ita ne tare da wani dan dan uwan Gwamnan, mai suna Ali Bello, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ranar Laraba, bisa zarginsu da badakalar kudin da suka haura Naira biliyan uku.

A cikin wata sanarwar da Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar ranar Laraba, ya ce an gurfanar da mutanen biyu ne da wasu mutum uku, bisa tuhume-tuhume 18 da suka jibanci halatta kudaden haram.

Sai dai bayanai sun nuna tuni matar Gwamnan ta cika wandonta a iska.

A cewar sanarwar, “Ana zargin kai Ali Bello da Abba Adaudu da Yakubu Siyaka Adabenege da Iyada Sadat da Rashida Bello (wacce yanzu haka ta tsere), da cewa wani lokaci a watan Yunin 2020 a Abuja, yankin da wannan kotun ke da hurumi, ku ka yi wata harkalla da wani kamfani mai suna E-Traders International Limited, wacce ta kai ta N3,081,804,654.00.

“Hakan dai ya saba wa doka kuma ba ya kan ka’ida, kuma a kan haka, kun aikata laifin da ya saba da sashe na 18(a), 15(20)(d) na Kundin Zambar Kudade na shekara ta 2011, wanda aka yi wa kwaskwarima a karkashin sashe na 15 (3) na shi dai wannan kundin,” kamar yadda takardar tuhumar da ake yi musu ta nuna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here