Gwamnatin Abia ta dakatar da nadin sarautar sarkin Hausawan Aba

0
106

Gwamnatin jihar Abia ta gargadi wasu gungun mutanen da ke shirin nadin Sarki Shehu Bello II a matsayin Sarkin Aba ba tare da izini ba kuma ba bisa ka’ida ba da su dakata ko kuma su fuskanci cikakken fushin doka.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Abia, Barr. Chris Ezem,  ya fitar ranar Laraba.

Ya bayar da umarnin soke nadin sarautar ba bisa ka’ida ba cikin gaggawa, inda ya kara da cewa babu wani abu kamar ‘Aba Emirate Council’ a jihar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Hankalin gwamnatin jihar Abia ya karkata ne kan batun nadin Sarki Shehu Bello na biyu a matsayin Sarkin Aba ba tare da sahalewar gwamnati ba.

“Gwamnati ta kara gargadin duk mazauna jihar musamman mazauna garin Aba da su kasance masu bin doka da oda.

“An umurci jami’an tsaro da su kara kaimi tare da tabbatar da cewa babu wani taron da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya da ake samu a jihar a Aba ko wani bangare na jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here