Tsoffin kudi: Gwamnati ta bukaci kotun koli ta yi watsi da hukuncin da ta yanke

0
106

Gwamnatin Tarayya ta bukaci Kotun Koli da ta yi watsi da karar da ke kalubalantar wa’adin da aka sanya na ranar 10 ga watan Fabrairu na daina amfani da tsofaffin kudi.

Babban Bankin Najeriya (CBN) wanda ya sauya fasalin kudin Naira, ya fara sanya ranar 31 ga watan Janairu 2023 a matsayin wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kudi.

Amma ya kara wa’adin zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu bayan matsin lamba da gwamnati da babban bankin suka sha.

A makon da ya gabata, Gwamnan CBN Godwin Emefiele, ya ce babban bankin ba zai kara tsawaita wa’adin ba.

Sai dai gwamnonin Jam’iyyar APC sun gana da Shugaba Buhari kan lamarin inda ya bukaci su ba shi kwanaki bakwai domin ya yi tunani kan lamarin.

A hukuncin da ya yanke ranar Laraba, kwamitin alkalai bakwai karkashin jagorancin Mai Shari’a John Okoro, ya dakatar da matakin na gwamnatin tarayya.

A karar farko da ya shigar a ranar Laraba ta hannun lauyoyinsa Mahmud Magaji da Tijanni Gazali, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Aminiya Shari’a, Abubakar Malami, ya ce kotun koli ba ta da hurumin sauraren karar.

Malami ya ce masu kara ba su bayyana dalilin daukar matakin kan wadnda ake tuhumar ba.

Sai dai sa’o’i kadan bayan hukuncin na kotu, Shugaba Buhari, da Emefiele da Malami, sun yi wata ganawar sirri a Fadar Aso Rock, kan batun canjin kudi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here