Hukumar NHRC za ta binciki ayyukan sojoji a Arewa maso gabas

0
100

Hukumar Kare ’Yancin Dan Adam ta Kasa NHRC ta kafa kwamitin binciki kan zargin take hakkin bil Adama da dakarun soji ke yi a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Hakan dai ya biyo bayan rahotanni da Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya wallafa tun a watan Disambar bara kan wannan batu na zargin take hakkin dan Adam da ayyukan dakarun soji ke haifarwa a Arewa maso Gabashin kasar.

Kwamitin wanda aka nada tsohon Alkalin Kotun Koli, Abdu Aboki a matsayin jagoransa, an kaddamar da shi ne ranar Talata a Abuja.

Sakataren NHRC Tony Ojukwu ya ce kwamitin zai binciko keta dokokin hakkin dan adam na kasa da na duniya ko akasinsu a ayyukan sojojin.

Ya kuma ce kwamitin zai tattaro bayanan ne daga al’ummomin yankin da kungiyoyi, musamman ma masu kiyaye hakkin dan adam da taimakon mutane da ke yankin.

Ojukwu ya kuma ce kwamitin na da hurumin mika duk wani lamari na take hakkin dan Adam da gurfanar da shi gaban babban lauyan kasa ko na jiha, tare da bai wa gwamnati shawarwari kan cibiyoyi, manufofi da matakan da ya kamata a dauka domin shigar da kiyaye hakkin dan adam cikin aikin soja a Najeriya.

Ya kuma tabbatar da adalci ga duk wanda sakamakon ya nuna an keta wa hakki, da kuma alkawarin tabbatar da gyara lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here