Yadda aka yi wa ‘yan Najeriya 16 kisan gilla a Burkina Faso

0
135

Kungiyar Jam’iyyatu Ansaariddeen Attijjaniyya (JAMAA) ta Nijeriya ta ce sojoji sun kashe ‘ya’yanta a Burkina Faso.

Da yake jawabi ga manema labarai a karshen mako a Abuja, Sayyadi Yahaya, sakataren kungiyar na kasa, ya ce an kashe ‘ya’yanta 16 ne a kan hanyarsu ta zuwa kasar Senegal.

Ya ce ‘ya’yan kungiyar a kai a kai suna ziyartar kasar Senegal, mahaifar shugabansu, Sheikh Ibrahim Niasse Al-Kaulahee, domin gudanar da taruka da bukukuwan Maulidi.

“A duk lokacin irin wannan taruka, ayarin motocin Nijeriya sun kasance suna bi ta kan iyakokin kasa da kasa zuwa Kaolack, Senegal, da ake bi ta kasashen Nijar, Burkina Faso, da Mali,” in ji Sayyadi Yahaya.

Ya ce sojojin kasar Burkina Faso ne dake gudanar da bincike suka tare tawagar ayarin ‘yan Nijeriya sannan suka saukesu daga motocinsu.

“Sojojin sun zabi wasu suka kyale wasu sannan suka harbesu ba tare da bayyana wani dalili ba. Adadin wadanda suka kashe a halin yanzu sun kai mutum 16, wasu motocin da mutanan ciki ba a san inda suke ba.”

Kungiyar Darikar Tijjaniyya ta bukaci gwamnatin tarayya da Majalisar Dinkin Duniya da su binciki lamarin tare da tabbatar da adalci.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan matafiyan da aka yi a kasar Burkina Faso.

A wata sanarwa da Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya fitar, Buhari ya ce ofishin jakadancin Nijeriya a Burkina Faso yana tattaunawa da hukumomin Burkina Faso don ganin an hukunta wadanda suka aikata laifin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here