‘Yan sanda sun kama wani da kokon kan mutum a Neja

0
141
CHICAGO, ILLINOIS - OCTOBER 19: Chicago police officers patrol downtown as the city celebrates the Chicago Sky's WNBA title on October 19, 2021 in Chicago, Illinois. The city has started to place police officers on unpaid leave for refusing to comply with the city's requirements that they report their COVID-19 vaccination status. Only about 65 percent of the city's police have complied with the order. (Photo by Scott Olson/Getty Images)

Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta kama wani mutum mai suna Abdulrahman Woru dan shekara 38 da ake zargi da yin tsafi da kokon kan mutum a garin Babana da ke karamar hukumar Borgu ta jihar.

Wanda ake zargin wanda ke zaune a Babana, dan kauyen Gbesewona ne na Jamhuriyar Benin.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakinta, DSP Wasiu Abiodun, ya sanyawa hannu a Minna.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 24 ga watan Junairu 2023 bisa ga wani rahoto da aka samu.

Ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a Babana bayan da ake zarginsa da mallakar kokon kan mutum.

A cewarsa, “A lokacin da aka gudanar da bincike a gidansa, an gano wasu kokon kan mutans guda uku, gumaka biyu da tsabar kudi CFA 5000 na kudin Jamhuriyar Benin.

“Lokacin da ake masa tambayoyi, ya amsa cewa kokon kan mutumin da aka gano nasa ne. Ya yi ikirarin cewa ya yi hijira ne daga Jamhuriyar Benin zuwa Nijeriya kimanin shekaru hudu da suka gabata don yin sana’arsa, ba tare da wata takardar shige da fice ba, kuma shi likitan gargajiya ne.”

“Shi (wanda ake zargin) ya ce ya daure shi ne a kan babur dinsa ya kai shi gida, saboda ya yi imanin cewa zai yi amfani da shi wajen aikinsa, kuma bai kai rahoto ga ‘yan sanda ba,” in ji kakakin ‘yan sandan jihar.

“Rundunar ‘yan sandan ta yaba da goyon bayan mutanen Neja kuma tana rokon su da kada su yi kasa a gwiwa ta hanyar sanar da ‘yansanda idan suka ga wani bakon abu.”

Nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban wata kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here