’Yan Arewa ba za su zabe ka ba, Adebanjo ya fadawa Tinubu

0
186

A ranar Asabar din da ta gabata ne jagoran wata kungiyar siyasa ta al’ummar kabilar Yarabawa ta Afenifere, Ayo Adebanjo, ya shawarci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, da ya janye takararsa ya marawa jam’iyyar LP ta Peter Obi.

Shugaban na Yarabawa ya bukaci Tinubu da ya ceci kansa daga kunyar da zai sha a zabe, yana mai cewa ’yan Arewa ba za su zabe shi ba.

Adebanjo wanda ya samu rakiyar wani shugaban kungiyar Afenifere, Sanata Femi Okunronmu, ya bayyana haka a taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar LP a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Adebanjo ya yi hasashen cewa ’yan Arewa za su butulcewa Tinubu a zaben.

Ya bayyana jam’iyyar LP a matsayin sabuwar amaryar jam’iyya wanda a cewarsa za ita  ceto ‘yan Najeriya daga mugunyar mulkin jam’iyyar APC.

Adebanjo ya ce, “Duk wanda ya san Tinubu ya fada masa, na sha fada masa kuma zan sake fada masa, ‘yan Arewa ba za su zabe shi ba.

“Ya kamata (Tinubu) ya dawo gida a yanzu ya marawa Obi baya domin a karshe idan suka ka da shi, ba zai samu karfin gwiwar dawowa gida ba, idan ya dawo yanzu, za mu yafe masa kuma mu maido da shi.

“Na sha fada muku a baya, kuma ina so in sake cewa, LP a yanzu ita ce , mu masu goyon bayan Obi ne masu son shugabanci na gari, muna son Najeriya ta inganta, muna son mu kwato kanmu daga hannun ‘yan adawa.

“Muna bayan Obi, shugabannin masu son ci gaba suna bayan Obi. Wadancan ‘yan damfara da suke nuna kansu a matsayin Yarabawa ba sa kaunar kasar. Yarabawa ba sa daukar abubuwan da suke na wasu kabilu.”

Tun da farko Obi ya kai ziyara ga Alake kuma mai mulkin Egbaland, Oba Adedotun Gbadebo, a fadarsa.

Da yake jawabi ga matasan a wani taro na gari da aka gudanar a harabar dakin karatu na Olusegun Obasanjo, Obi ya bayyana Najeriya a matsayin  daya daga cikin kasashen da ba su da tsaro a duniya “wacce ba ta da iko da yankinta a yanzu”.

Ya ce, “A gare ni, na yi wa al’ummar Jihar Anambra hidima kuma na ba ni matsayi na daya wajen aiwatar da muradun karni kuma bayanan suna nan. Ko a fagen ilimi da fitar da mutane daga kangin talauci ba tare da aron Kobo daga kowa ba; Na biya duk kudaden fansho da ake bina kafin in bar ofis.

“Don haka, a bar ‘yan takarar shugaban kasa su fito su nuna wa ‘yan Nijeriya abubuwan da suka yi a baya kafin su yi yunkurin mulkin kasar nan.

“Mun kuduri aniyar samar da sabuwar Najeriya. Muna son mutanen da suke da tabbaci, kuma waɗanda suka cancanci aikin. Zaben na bana yana da matukar muhimmanci, ba za mu iya samun kwanciyar hankali da rashin cancanta ba. Muna son mutanen da za su nuna himma; wannan aikin yana buƙatar lafiyar jiki da na tunani. Don haka, muna son mutanen da suke shirye don aikin. Ni da Datti mu na son canza Najeriya.

“Ni da Datti muna son mu canza Najeriya; mu kadai ne mutanen da za su iya yin hakan. Muna da karfin yin hakan, shi ya sa muke cewa ku ba mu amanar kasar, kuma za mu mayar da ita babbar kasa. Ku ɗora mana alhakin magance wannan al’amari.

“Najeriya babbar kasa ce, amma duk mun bar ta ta kasance a hannun ‘yan tsirarun da ba su san yadda ake tafiyar da ita ba, shi ya sa muka zo nan domin neman albarkar ka. Mun san ba wani uban sarauta da ke shiga siyasa, amma idan talakawanku suna mutuwa, idan kuma ba ku shiga tsakani ba, wata rana za su zo muku domin babu wata mafita, don Allah ku cece su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here