Daliban makaranta sun kai wa ‘yan sanda hari bayan kashe abokin karatunsu

0
135

Wasu dalibai a lardin Free State na Afirka ta Kudu sun yi wata tarzoma a ranar Alhamis bayan da labarin mutuwar wani dan makarantarsu, lamarin da yasa har suka juya wata motar ‘yan sanda har suka jrikitar da ita a gefenta.

Wani rahoton jaridar intanet mai suna Times Live, ya nuna cewa dan makarantar ya kashe kansa ne a sanadiyyar muzgunawar da wani malami ya rika yi masa.

‘Yan sandan yankin sun sanar cewa, “Dalibin ya bar wata wasika da ke cewa malamin ne yayi sanadin kashe kansa da yayi.”

Bayyanar labarin mutuwar dalibin ya sa ‘yan makarantar “su tunzura kuma suka fara lalata kayayyakin makarantar”, kamar yadda jami’in ‘yan sanda Warrant Officer Peter Mabizela ya sanar.

Daga nan ne dalibai daga makarantun da ke kusa suka tarua makarantar sakandare ta Tlotlisong, inda suka yi garkuwa da wasu ‘yan sanda biyu da malaman makarantar cikin wani daki.

Daliban sun kuma kai wa motar ‘yan sandan hari, inda suka juya ta zuwa gefenta. Sai dai aka tura karin jami’an ‘yan sanda sannan aka kwantar da tarzomar daliban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here