Kashi 50 na magungunan Afrika jabu ne

0
111

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar sama da kashi 50 na magungunan da ake sayarwa a kasashen Afirka ta Yamma marasa inganci ne, abin da ya sa sukan bijire wa cututtuka da kuma sanya mutane rashin amincewa da tsarin kula da lafiyar da ake amfani da su.

Ofishin majalisar da ke kula da magunguna ya ce tsakanin watan Janairun shekarar 2017 zuwa Disambar shekarar 2021 akalla tan 605 na irin wadannan magunguna marasa inganci aka kwace a yankin daga masu safarar su.

Majalisar ta ce a kowacce shekara ana kashe kudin da ya kai kusan Dala miliyan 45 wajen kula da lafiyar jama’ar da suka yi amfani da irin wadannan magunguna marasa inganci a matsayin maganin cutar zazzabin cizon sauro, yayin da ake samun mutane dubu 267 da ke mutuwa kowacce shekara saboda kwankwadar magungunan.

Bayan magungunan marasa inganci, majalisar ta yi kuma gargadi akan yadda ake amfani da wasu magunguna ta hanyoyin da ba su kamata ba, abin da ke haifar da bijirewar wadanda ake amfani da su wajen kare kai daga cutar zazzabi.

Francois Patuel, shugaban sashen bincike da kula da magungunan Majalisar yace ba’a iya sanya ido wajen ganin yadda ake amfani da magungunan da zaran sun bar kamfanonin da aka sarrafa su.

Rahotan wanda ya mayar da hankali akan safarar magungunan ta barauniyar hanya ta kasashen Mauritania da Mali da Burkina Faso da Nijar da kuma Chadi ya ce ana karkata su ne daga Turai da China da kuma India, yayin da suke bi ta gabar ruwan kasashe irinsu Guinea da Ghana da Togo da Benin da kuma Najeriya zuwa yankin Sahel baki daya.

Majalisar ta ce mutanen da suke amfana da safarar wadannan gurbatattun magunguna sun hada da ma’aikatan kamfanonin da ake sarrafa su da jami’an tsaro da kuma masu sayar da su akan tituna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here