Shin ko kunsan tsibirin da aka hana kowa zuwa a duniya ?

0
624
north sentinel island
north sentinel island

Shi wannan guri Mai suna North Sentinel Island an aka hana kowa zuwa yana da nisan kilomita 1300 daga kasar India sannan yana da da nisan kilomita 300 daga kasar Myanmar. Shi wannan tsibiri yana tsakiyar ruwa sannan duk nisansa da india tsibirin ya fada cikin yankin India.

Shi wannan tsibiri an fara zuwansa a 1867 dalilin fara zuwa gurin kuwa shi wani jirgin india ne ya daki gabar tsibirin yai hatsari inda jirgin ya lalace shi ne mahayan jirgi suka shi ga cikin tsuburin.

Shigarsu wajen baifi da minti biyar ba aka fara Kai musu hari ba zato ba tsammani kuma basu ga kowa ba sai jin ruwan kibiyoyi kawai sukai to allah yasa jirgin nasu guda biyu daya ne ya samu matsa suka zauna gyaransa shi ne sukai sauri suka hau jirgin suka gudu.

Bayan tafiyarsu suka sanarwa da hukuma abinda ya faru da kuma sanar da hukumar kasar ta India dai dai inda abin ya faru.

Duk da hukuma ta samu labarin abinda ya faru gwamnatin india bata dauki wani mataki ba sai 1970 in da kasar ta India ta nemi goyon bayan kasashen da suka yi nisa wajen bincike domin aje gurin a gano hakikanin abinda ke faruwa a gurin wanda yunkurin hado kan masu binkicen ya dauki zawon shekara hudu sannan aka je gurin.

Stunk afin su karasa ciki aka fata yi musu ruwan kibiyo kafin su kara duk sun kashe su.
Ganin abinda ya farau yasa gwamnatin indiya bata kara tura kowa ba sai sai a shekarar sai 1991 lokacin an samu karin samu cigaba da kimiyya da fasaha inda aka je gurin a helicopter sannan aka. Tafi musu da kayayyakin abinci da sauran kayan anfani.

Zuwan su ke ka wuya suma aka bude musu wuta da ruwan kibiyoyi ko ya ina inda suka kashe su ko daya ba wanda ya dawo da ranshi saboda kafin su shirya sun cin musu.

To shi ne a lokacin aka gano mutanen da suke cewa akwai mutane a tsibirin kuma bakaken fata ne sai duk da dai haryanzu ba Kai ga gano wane kabilarsu ba su saboda lokacin da mutanen suka bakin sun shigo suka fara gudu suna komawa cikin daji.

Gwamnati tun daga wannan lokacin ba ta kara bibiyar zuwa gurin ba sai a 2006 wani abin al’ajabi ya faru lokacin da wasu masu kamun kifi da daddare ke cikin kamun kifi sai barci ya kwashe su gaba daya kwalekwalensu kuwa yai ta tafiya dasu har ya Kai su ga bakin wannan tsibiri.

Isar kwalekwalen ke da wuya kafin ka ce me, mutanen tsibirin sun kashe su. Faruwar hakan ne yasa aka tafi da helikofta domin nemo wadannan gawarwakin zuwan jirgin kenan mutanen nan suka farwa jirgin suka baro shi dun daga wannan lokaci aka hana kowa zuwa wajen har kawo yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here