Chelsea ce mafi kashe kudi a kasuwar musayar ‘yan wasan Firimiya ta bana

0
93

A daren jiya talata ne aka kammala kulle kasuwar musayar ‘yan wasa ta kasashen Turai inda kungiyoyi da dama suka yi ciniki mai tsoka ciki har da wadanda aka kammala sa’o’I kalilan gabanin kulle wannan kasuwa, cikin wadannan ciniki har da Chelsea da ta sayo Enzo Fernandez na Argentina daga Benfica kan yuro miliyan 121 wanda ya zama dan wasa mafi tsada da wata kungiyar firimiya ta sayo daga waje.

Cinikin na Fernandez ya danne surutun da ake kan yadda Manchester City ta zuba har yuro miliyan 100 wajen sayen Jack Grealish a shekarar 2021 wanda a wancan lokaci ya zama dan wasa mafi tsada.

Dukkanin kungiyoyin biyu dai sun fitar da sanarwar kammala sayen matashin dan wasan wanda Benfica ta saya a watan Agustan bara kan yuro miliyan 10 amma kuma farashinsa ya yi wannan irin linkuwa.

Bisa al’ada rawar da dan wasa ya taka a manyan gasa musamman na kasa da kasa su ke taimakawa wajen daga darajarsa, lamarin da ya faru da Enzo wanda kasar shi ta lashe kofin Duniya kuma anga rawar da ya taka wajen kai kofin Argentina inda har ya zama matashin dan wasa mafi bajinta gasar cin kofin duniya da ta gudana a Qatar.

Cinikin dan wasan mai shekaru 22 ya mayar da adadin kudin da Chelsea ta kashe a kasuwar musaya zuwa yuro miliyan 288, bayan sayen Noni Madueke da Mykhailo Mudryk da kuma David Datro Fofana baya ga Andrey Santos da Benoit Badiashile da kuma Malo Gusto baya ga aron Joao Felix daga Atletico Madrid.

Haka zalika tuni matashin dan wasan na Argentina ya shiga sahun ciniki mafi tsada da aka gani a Turai kwatankwacin na Antoine Griezmann da Barcelona ta biya yuro miliyan 120 akansa cikin shekarar 2019.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here