Alkaluman wadanda harin Masallacin Pakistan ya kashe ya kai 83

0
100

Alkaluman mutanen da suka mutu a harin kunar bakin waken da aka kai Masallaci a Pakistan ya karu zuwa 83 ciki har da tarin jami’an ‘yansanda yayinda wadanda suka jikkata suka karu zuwa fiye da mutum 50.

An kai harin ne a lokacin da jama’a suka hallara domin gudanar da Sallar Azahar a Masallacin da ke shalkwatar Jami’an ‘yan sandan Pakistan a birnin Peshawar da ke kusa da kan iyakar Afghanistan mai fama da ayyukan ta’addanci.

Yanzu haka ana ci gaba da aikin agaji a Masallacin wanda daukacin garunsa da rufinsa suka tarwatse a dalilin karfin fashewar da ta auku a yayin farmakin.

Shugaban Rundunar ‘Yan sandan Peshawar, Mohd. Ijaz Khan ya ce, kimanin jami’an ‘yan sanda 300 zuwa 400 ke yawan halartar Masallanci a kullum, kuma buraguzai sun danne da dama daga cikinsu a sanadiyar harin na yau.

Motocin Asibiti sun yi kwasar gawarwakin mutanen da suka rasu, sannan an ga yadda wadanda suka tsira da rayukansu ke ta dingisawa bayan sun yi jina-jina sakamakon buraguzan da suka fado musu.

Tuni dai hukumomi suka sanya kasar cikin gagarumin shirin-ko-ta-kwana bayan wannan harin na bam, inda aka zafafa bincike a shingayen ababen hawa tare da jibge karin jami’an tsaro a wasu wurare.

Kazalika an girke jami’an tsaro na musamman da suka kware wajen harbi da bindiga a babban birnin Islamabad.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here