Ina addu’ar Allah ya saukar min da cutar da za ta sa na shiryu – Murja Ibrahim Kunya

0
183
Murja Ibrahim Kunya
Murja Ibrahim Kunya

Fitacciyar mai barkwancin nan ta manhajar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, ta bayyana cewa ta yi saukar Qur’ani amma bata kammala karatun sakandire ba.

Murja, mai shekara 24 a duniya, ta bayyana hakan ne a lokacin da take amsa tambaya ga rundunar ‘yan sandan jihar Kano.

Matashiyar ta bayyana cewa zagin da ake zargin cewa ta yi tsoho ne kuma ta dade da yi sannan kuma tana fatan daina zage-zage a shafin na ta na TikTok.

“Wasu mata na gani a daji ana dukansu shi ne hankali na ya tashi, mun yi kira domin a sako su amma abin ya gagara shine na fito na yi zagi sannan zagi na biyu kuma wani ne ya yi fostin cewa na yi hatsari na mutu hankalin mahaifiya ta ya tashi hakan yasa na yi zagin” in ji Murja, ‘yar asalin unguwar Hotoro da ke jihar Kano.

Da aka tambaye ta akan maganganun da take yi na batsa a shafin nata, sai Murja ta ce “Wakokin Ado Isa Gwanja ne guda biyu na “Warr” da “Chass” kuma itama gani ta yi ana bin wakar sannan ta yi amma bata san wakar ta sabawa doka ba.

“Tun mutuwar Kamal Aboki na yi addu’ar Allah ya kawo min cutar da za ta yi sanadiyyar shiriya ta” Cewar Murja.

Zauren hadin kan malaman jihar Kano ne dai ya shigar da karar Murja inda yake zarginta da furta kalamai na rashin tarbiyya da suka sabawa addinin musulunci wanda kuma zai iya zama hatsari ga ‘yan baya.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewa kwamishinan ‘yan sanda ya bayar da damar a kai Murja asibiti domin a duba lafiyar kwakwalwar ta.

Kuma da zarar an kammala bincike za a sanar da mataki na gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here