Daga 2016 zuwa 2020, an kashe dala biliyan 6 wajen shigo da alkama – CBN

0
100

Wani rahoton da babban bankin Nijeriya CBN ya fitar, ya nuna cewa, yawan adadin alkamar da aka shigo da ita daga kasar waje daga shekarar 2016 zuwa shekarar 2020, an kashe kimanin dala biliyan shida.

A cewar rahoton, wannan ba za ta sabu ba,  musamman ganin cewa,  za a iya nomanta da yawa a kasar nan.

Bisa wasu alkaluman da aka samo daga gun   hukumar kididdiga ta kasa NBS ta bayyana cewa, kudaden da aka kashe wajen shigo Alkamar daga waje a cikin zango uku na shekarar 2022 sun kai kashi 16.1 a cikin dari,  inda wannan ya nuna cewa, kudaden sun kai kasa da wanda aka kashe a shekarar 2021.

Jimmlar naira biliyan 753.597 aka yi amfani da su wajen shigo da Alkama daga kasar waje zuwa cikin kasar nan a cikin watanni tara da suka gabata a shekarar 2022.

Wannan ya nuna cewa,  kasar ce ke akan gaba wajen shigo da Alkamar daga ketaren.

Har ila yau, Alkamar ita ce ta uku wajen amfanin gona zuwa cikin kasar nan baya ga man fetur.

Akasari dai, ana da matukar bukatar Alkama a cikin kasar nan,  musamman ganin yadda ake yin da ita wajen sarrafa nau’ukan abinci da ban da ban a kasar.

Bugu da kari, a cikin zango na uku ma shekarar 2022 Alkamar da aka shigo da ita daga ketaren zuwa cikin kasar nan,  bata kai yawan kudaden da aka kashe wajen shigo da sauran amfanin gona cikin Nijeriya ba

Hakazalika,  a zangon farko na watanni uku 2021, an kashe naira biliyan 898.19 da kuma naira biliyan 258.3 don shigo da ita daga ketaren.

A zangon farko na shekarar 2021 an kashe naira biliyan 324.72 da kuma kashe naira biliyan

315.17 don shigo da sauran kayan abinci,  nda kuma a zango na biyu da na uku na shekarar 2021.

Bugu da kari, a 2022  an kashe naira biliyan 258.31 da kuma naira biliyan 242.66 tare da kashe naira biliyan 252.62 don a shigo da Alkamar daga ketaren.

Har ila yau,  a shekarar 2021 jimmalar Alkamar da aka shigo da ita daga waje zuwa cikin kasar nan, kudin da aka kashe ya kai naira tiriliyan 1.29, inda hakan ya kai karuwar kashi 71.1 a cikin dari idan aka kwatanta da naira biliyan 756.92 da aka kashe a 2020.

Hakazalika, sakamakon yakin da kasar Rasha ke ci gaba da yi da kasar Ukraine, haka ya kara haifar da hauhawan farashin na Alkamar a daukcin fadin duniya.

An ruwaito cewa ministan akin noma da raya karkara Mahmood Abubakar ya bayyana cewa, ganin,yadda yawan al’ummar kasar nan ke kara karuwa da kuma yadda ake kara ci gaba bukatar ta Alkamar a kasar, akwai bukatar a kara yawan yin nomanta a kasar don a samar da wafatacciyar ta.

A cewar ministan,  gwamnatin tarayya na ci gaba da mayar da hankali a fannin na nomanta,  inda ya kara da cewa, a duk shekara Nijeriya na bukatar kimanin tan miliyan  5.7, inda kuma yawan adadin tan, 420,000 kawai ake iya noma wa a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here