Jirgin kasa dauke da fasinjoji ya kauce hanya tsakanin Abuja zuwa Kaduna

0
92

Bayanai daga Najeriya sun bayyana cewa jirgin kasa da ke jigilar fasinja daga Abuja zuwa Kaduna, ya kauce wa hanyarsa a wannan juma’a daidai lokacin da ya isa a Kubwa, lamarin da ya haddasa tseko ga daruruwan fasinjoji da ke cikin jirgin.

Shugaban Hukumar Jiragen kasa a Najeriya NRC Inginiya Fidet Okhiria ya tabbatar da faruwar hadarin, to sai dai ya ce suna ci gaba da bincike domin tantance dalilan faruwar lamarin ba.

Wannan hadari dai ya faru ne kasa da mako daya bayan bayan da wani jirgin daukar fasinja ya kauce wa hanyarsa a layin dogon da ya tashi daga Itakpe zuwa Warri a cikin jihar Kogi da ke tsakiyar kasar.

To sai dai wasu bayanai na nuni da cewa ga alama jirgin ya kauce wa hanyarsa ne sakamakon zagon kasa, ko dai daga masu satar kwangiri domin sayarwa ko kuma tsageranci.

Dubban mutane ne ke amfani da jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna a matsayin hanyar sufuri domin zuwa yankin Arewacin Najeriya, duk da cewa watanni 9 da suka gabata, ‘yan ta’adda sun dasa bam wanda ya tarwatse a lokacin da jirgin ke wucewa dauke da fasinjoji kusan 900.

Daga bisani dai ‘yan ta’addar sun yi awun gaba da wasu fasinjojin, yayin da suka kashe wasu a lokacin harin, lamarin da ya tilasta dakatar da jigiliar jiragen kasa a wannan hanya tsawon watanni 8.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here