Masu kudi su ajiye kudinsu, zan bawa kowa damar canzawa a hankali idan naci zabe – Kwankwaso

0
185
Rabiu-Musa-Kwankwaso-
Rabiu-Musa-Kwankwaso-

Ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce baya goyon-bayan tsarin da aka bi wajen sauya takardun kuɗi a Najeriya.

Kwankwaso da ke shaida hakan a lokacin wata tattaunawa da BBC, ya ce yanzu abu guda shi ne mahukunta a kasar su kokarta su kara wa’adin da babban bankin kasar ya bayar na daina amfani da tsoffin takardun kuɗi.

Injiniya Kwankwanso ya ce al’umma na shan wahala sakamakon canjin kuɗin, don haka ya kamata gwamnati ta sassauta

Kalaman ɗan takaran na zuwa ne kwanaki kadan wa’adin da babban bankin Najeriya wato CBN ya bayar na daina karban tsoffin kuɗi ya cika.

Sai dai dan takarar ya ce idan gwamnatin APC mai Mulki ta ƙi kara wa’adin, kada kowa ya ta da hankalinsa.

Injiniya Kwankwaso ya ce masu kuɗi su ajiye kudinsu, idan ya samu nasarar zama shugaban  kasa zai bai wa kowa damar canja kuɗinsa ba tare da kwabonsa ya yi ciwon kai ba.

BBC

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here