An zargi Masari zai kashe miliyan 500 don tarbar Buhari a Katsina

0
104

Jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Katsina, ta zargi Gwamnan Jihar, Aminu Bello Masari, da bayar da umarnin kashe sama da Naira miliyan 500 daga asusun kananan hukumomin jihar don tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa jihar.

Ana sa ran Buhari zai kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu, daga ranar 26 zuwa 27 ga watan Janairu a jihar.

Sai dai jam’iyyar adawa ta PDP a jihar ta soki wannan shiri, inda ta alakanta da shi a matsayin almubazzaranci.

Shugaban kungiyar yada manufofin Atiku da Lado, Alhaji Lawal Ɗan Ade ya yi zargin cewa za a kashe kudaden ba bisa ka’ida ba.

Alhaji Lawal Dan Ade, ne ya shaida wa manema labarai cikin wata takarda da ya ce gwamnan jihar, ya amince tare da sahale kashe kudaden.

A cewarsa takardar wadda aka turawa Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar, ta nuna cewa za a cire miliyan N14,695,588.00 daga kowace karamar hukuma.

Adadin kudin da za a cire daga jihohin baki daya zai kai kimanin Naira miliyan N499,650,000.00

“Idan har wannan zargi da muke yi, ya tabbata muna kira da babbar murya cewa Katsinawa su fito su nuna rashin amincewarsu kan wannan badakala da aka shirya domin zuwan shugaba Buhari Jihar Katsina” in shi

Ya kuma kara da cewa ya kamata shugaba Buhari, ya nesanta kansa da wannan badakala da ake shirin aikatawa a jihar.

A cewarsa wadannan kudede akwai abubuwa da yawa da za a iya da su musamman wajen magance matsalolin da suka shafi makarantu da asibitoci da ‘yan gudun hijira da sauransu.

Sai dai Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na Jihar Katsina, Ya’u Umar Gwajo-gwajo, ya musanta wannan zargi, inda ya ce har yanzu idonsa bai ga wannan takarda da ake magana ba.

Kwamishinan ya sha alwashin bin diddigin wannan takarda da ake zargin an cire wadannan kudade.

Ya ce zai bayyana abin da ake ciki game da maganar kudaden.

“Kamar yadda na fada cikin satin da ya gabata cewa kudaden kananan hukumomi suna nan ba gara ba zago, to har yanzu sunan nan, babu wata magana kan cewar za a cire wasu kudede domin zuwan shugaban kasa Jihar Katsina,” in ji shi.

Ana sa ran shugaba Buhari zai kai ziyarar ne don bude wasu manyan ayyuka da gwamnatin jihar ta yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here