Bayan Kamal Aboki, masana’antar Kannywood ta kara rashin jarumi Awarwasa

0
123

Kwanaki kadan bayan rasuwar fitaccen dan wasan barkwanci Kamal Aboki, yau yammacin litinin wani rashin ya sake afkawa  masana’antar ta Kannywood. Yayin da Abdulwahab wanda aka fi sani da Awarwasa ya rasu

Wata majiya me tushe ta sanarwa jaridar Hausa24 cewa wannan jarumi ya rasu ne bayan wata gajeriyar rashin lafiya da ya kwanta.

Ya kara da cewa, a makon da ya gabata jarumi Awarwasa ya kammala wani shirinsa da yake aiki akai sai dai bayan kwana biyu ya yanke jiki ya fadi bayan ya fito daga motarsa. Wanda daga nan sai jin labarin rasuwar sa akaji.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here