Dabi’un dan wasan da nake koyi dashi – Pogba

0
106

A cikin wata hira mai zurfi da Sky Sports don murnar Watan Tarihin Bakar fata, tsohon dan wasan tsakiyar Manchester United Paul Pogba ya yi magana game da gwarzonsa Muhammad Ali da yadda fitaccen dan dambe ya taimaka wajen daidaita rayuwarsa zuwa yanzu.

Pogba ya yi magana ta zahiri game da cin zarafin wariyar launin fata da iyayensa suka jure da kuma dalilin da ya sa ya kuduri niyyar kawo canji. Haka kuma Pogba ya bude bayannan hanyar kasancewar kyawun rayuwarsa a Musulunci a dalilin gwaninsa Ali.

Yan wasan kwallon kafa su kan zama fitattu ne a duniya tare da samun miliyoyin kudade, amma su kan bayyana shin wanene gwarzonsu?

Shin wanane Gwarzon Pogba “Muhammad Ali?. Ya kasance wani mutum wanda nake tsammanin yana ceton rayuka. Jarumi shi ne wanda ke ceton rayuka, yana taimakon mutane, kuma ina tsammanin abin da yake yi kenan. Ya ceci mutane da yawa, amma kawai ta hanyar ba da sako mai kyau, ya taimaka wa duniya, fadin gaskiya lokacin da wuyane fadin ta a lokutan da suka kasance masu wahala ga bakar fata. Ya yi magana ga bakar fata kuma ya taimaka mana mun sami ‘yanci a yau,” in ji Pogba ”

“Wannan shi ne dalilin da ya sa ya zama gwarzo, abin koyina. Babu shakka, Na fuskanci lokaci ne mai wahala kamar yadda kuke tsammani kuma iyayena sun kasance suna gaya min tarihin abin da ya yi wa bakar fata.

Ya kasance gwarzo. Haka nan, shi mutum ne mai hikima ina mai baku shawara kuma kuna kokarin yin koyi da wannan mutumin. ”

Shin iyayenku sun taba yi muku magana game da Muhammad Ali musamman, ko kuma game da rayuwa shekaru 40 ko 50 da suka gabata?

“Mahaifina, lokacin da ya isa Faransa, a lokacin da ya gaya mani cewa an kai masa hari kuma mutane sun gaya masa wasu kalaman wariyar launin fata masu sanya zafin rai da matukar damuwa lokacin da yake cikin motar bas.

Pogba ya kara da cewa Mahaifina ko yaushe yana gaya min in kasance cikin nutsuwa da wayo, kawai in kyale masu yi min kalaman wariya, in zama mai hankali fiye da wadancan mutanen, don haka kawai kar na rika basu amsar maganarsu. Na san ko wanene ni, dole ne in yi alfahari da yadda nake, koyaushe. Ina alfahari da launin fatata. ”

Me kuke tunani game da yadda Muhammad Ali ya kasance jarumi don yin magana a lokacin yana a Amurka?

“Ina tsammanin kamar ba za mi iya yin magana mai sanya kwarin gwiwa kamar yadda yadda yake iya shigar magana, tare da azanci ba, shi ya kasance mutum ne mai azanci, yana da hikima sosai kuma ya san yadda ake aika sako amma ba tare da rigima da wani ba, saboda mutane ba za su ce yana neman rigima ba’,

Shi Muhammad Ali Yana da tausa murya, hali nagari, kwarjini, kan fadar komai ta hanyar wasa, ko ta wata hanya mai kyau da basira, don haka mutane za su fahimta kuma ba za su yi fushi ba. ”

“To, ina fatan haka saboda zan iya cewa na koyi kadan daga gare shi, yadda za ku kasance da yarda da kawunanku za su kasance a hade. Wannan wani abu ne da ba zan iya canzawa ba. Ina son murmushi, wasa, dariya da rawa. Wannan shi ne abin da na fahimta, sannan kuma ina son zama mai ra’ayin kaina.

Haka nan, shi mutum ne wanda ba ya cuta kuma ni ma bana cuta, don haka yana da ban sha’awa a gare ni in san labarinsa. Kowa yana da tarihin kansa don haka ina sha’awar sanin halayyarsa. ”

Juyowa hankalin wasu zuwa Musulunci, daga abin da kuka karanta kuma kuka gani, me kuke tunani, hakan ya zama mafi alheri da kyau a gare shi, ta yadda yake gudanar da lamarinsa cikin nutsuwa

“Ina tsammanin na dauki wasu kyawawan halayensa, me yiwuwa ku iya tambaya cewa me ya sa hakan ya faru da ni, me ya sa wannan abin ya zo min haka, me ya sa hakan.

In kuma sai in ce muku Musulunci ne ya ba mu wannan, a Al -Kur’ani mai girma ya ba ni hanyar da zan zama jagoran rayuwata, da yadda komai ya kan iya kasancewa da ni tar da sanin me ya sa ma muke a cikin wannan rayuwa.

A dalilin hakan idanuna sun bude sosai game da sanin rayuwa, da komai, da kuma sanin muhimman abubuwa, fiye da kwallon kafa kuma fiye da dukkan wasanni, ba don saiti irin addinin Musulunci ta yaya za mu fahimci rayuwa, lallai ba za mu fahimci abubuwa da dama ba domin cewa komai mukaddari ne, don haka kaddararku ita ce makomarku, ba za ku iya canza hakan ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here