APC da PDP na zargin juna da aikata miyagun laifuka

0
99

Yayin da Najeriya ke shirin gudanar da zaben shugaban kasa a watan gobe, yanzu haka magoya bayan ‘dan takarar Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da magoya bayan ‘dan takarar Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar na ci gaba da zargin juna akan aikata manyan laifuffuka lokuta daban-daban.

Jam’iyyar APC ta zargi Atiku da jagorantar almundahana lokacin da yake rike da mukamin mataimakin shugaban kasa a karkashin gwamnatin Olusegun Obasanjo, wadda ta ce ya ba shi damar satar kudaden talakawa tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.

Wannan ya sa ‘dan takara Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Atikun da ya janye daga takarar zaben da kuma ya gabatar da kansa wajen hukumomi domin kare kansa.

Magoya bayan PDP sun bayyana Bola Tinubu a matsayin wanda kwaya ta yi wa illa da kuma wanda aka taba samu da laifin safarar kwayoyi a Amurka, zargin da jam’iyyar APC ta musanta.

Har ila yau PDP ta zargi Tinubu da kafa rundunar ‘yan bindiga wadanda za su yi wa shirin zabe mai zuwa zagon kasa, inda suka bukaci kama shi domin amsa tambayoyi daga hukumomi.

PDPn ta kuma bayyana cewar Tinubun ba ya iya tsayawa mike, kana baya iya hawa bene sai da taimakon jama’a saboda yadda jikinsa ke rawa sakamakon rashin lafiya.

Wannan zargi ya sa magoya bayan Tinubu gabatar da wani faifan bidiyo mai dauke da ‘dan takarar yana tikar rawa da kuma hawa keken motsa jiki.

Yanzu dai haka kakakin yakin neman zaben Tinubu, Festus Keyamo ya maka hukumar EFCC da ICPC da kuma hukumar kula da da’ar ma’aikata a gaban kotu, inda yake bukatar da su tuhumi Atiku akan zargin da ake masa na karkata wasu kudade lokacin da yake rike da mukamin mataimakin shugaban kasa.

Daukar wannan mataki ya biyo bayan cikar wa’adin sa’oi 72 da Keyamo ya bayar na gayyatar Atikun wanda ya cika ba tare da daya daga cikin hukumomin ta yi ba.

Ministan ya bukaci haka ne bayan da aka ruwaito wani tsohon hadimin Atikun da ake kira Michael Achimugu ya saki wasu bidiyo da ke dauke da zarge-zarge da dama akan tsohon mai gidansa.

Bisa dukkan alamu, magoya bayan wadannan ‘yan takara za su ci gaba da amfani da sauran lokacin da ya rage na gudanar da zaben domin batanci a tsakaninsu, ganin yadda kowanne bangare ke zargin juna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here