Za a fara kidayar ‘yan Najeriya a watan Maris – NPC

0
108

Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC), ta ce za a gudanar da kidayar jama’a a fadin kasar nan na shekarar 2023 daga ranar 29 ga Maris zuwa 2 ga Afrilu.

Shugaban NPC, Nasir Kwarra ne, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ganawarsa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaban NPC ya ce “A ranar 29 ga Maris zuwa 2 ga Afrilu, ma’aikatanmu za su kasance a fagen daga don kidayar mutane.”

Kwarra ya yi alkawarin cewar aikin zai sha bamban da na baya domin za a gudanar da shi ne da fasahar zamani.

Da yake tabbatar da hakan, shugaban NPC, ya jaddada cewa kidayar za ta kasance mafi inganci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here